19 Afirilu 2021 - 14:48
An Tsaida Ranar Zaben Shugaban Kasa A Siriya

Majalisar dokokin Siriya, ta tsaida ranar 26 ga watan Mayu mai zuwa a matsayin ranar da za’a kada kuri’a a zaben shugaban kasar.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan a wani taron majalisar dokokin kasar na gaggawa, shugaban majalisar Siriyar, Hammouda Sabagh, ya ce za’a fara ajiye takara a zaben shugaban kasar a ranar Litini mai zuwa.

‘Yan Siriyar dake ketare su kuma zasu kada kuri’a a ofisohin jakadancin kasar a ranar 20 ga watan na Mayu.

Zaben shugaban kasar dake tafe a Siriya shi ne irinsa na farko cikin shekaru 10 tun bayan da kasar ta fada cikin rikici.

342/